Gwomna Bala Muhammad tare da Gwomnonin PDP Sun Halarta Taron Gala a Asaba a yammacin yau
Gwamnonin jam’iyyar PDP da suka hallara a Asaba domin taron PDP Governors’ Forum sun halarta wata kyakkyawar liyafa ta Gala Night/Dinner da mai masaukinsu, Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, ya shirya. Taron ya kasance cike da ado da nishaɗi, tare da gabatar da wasannin al’adu masu kayatarwa da ke nuna arzikin al’adun Jihar Delta.
A jawabinsa na buɗe taro, Gwamna Oborevwori ya tarbi baki da hannu biyu, yana mai nuna farin cikinsa da karɓar irin wannan babbar tawaga ta manyan shugabanni. Ya yi addu’ar samun nasarar taron da ke tafe tare da jaddada sadaukarwar Jihar Delta ga manufofin jam’iyyar PDP.
Shima da yake jawabi, Shugaban PDP Governors’ Forum, Gwamna Bala Mohammed, ya yabawa Gwamna Oborevwori bisa ci gaban da ya kawo a Jihar Delta. Ya jinjina wa ayyukan raya ƙasa da ke gudana a jihar, yana mai bayyana Delta a matsayin “fuskar PDP a Najeriya.” Haka kuma, Gwamna Bala Mohammed ya jaddada muhimmancin haɗin kai da aiki tare don ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓukan da ke tafe.
Suleiman Musa Konkiyel,
Special Assistant on Communications to His Excellency,
30/01/2025.