GWAMNAN BAUCHI DA MUƘARRABAN GWAMNATINSA SUNYI TA’AZIYA WA IYALAN MARIGAYI SANI GALAJE (GALAJEN KAURA)

A Ranar Laraba 22 ga wannan wata ne Allah yayi rasuwa wa Sani Abdulhamid Galaje ( Galajen Ƙaura)

Yayin da a wannan Alhamis Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya jagoranci tawagar Muƙarraban gwamnatinshi suka gabatar da ta’aziya wa Iyalan gidan Galaje a kan Titin Kofar Ran dake cikin garin Bauchi bisa Rashin Sani Abdulhamid Galaje.

Da yake jawabi Gwamna Bala Abdulƙadir Muhammad ya bayyana Marigayi Sani Galaje ne a matsayin Matashi mai hakuri wanda ya bada gudumawa wajen kawo gwamnatinshi amma Allah baisa zai ga ƙarshen gwamnatin ba.

Gwamnan yayi Addu’ar Allah ya gafarta mishi ya bayar wa iyalen Marigayin hakuri da juriyar rashi.

Da yake mai da jawabi a madadin Iyalai Galajen Bauchi Alh. Adamu Abba yayi godiya tare da fatar Allah ya bayar wa gwamnan da Muƙarrabanshi ladar ta’aziya,

Gwamnan ya sami rakiyar Mataimakin shi RT Hon Muhammad Auwal Jatau, Shugaban jam’iyyar PDP Pharm. Sama’ila Adamu Burga da Mambobin Majalisar Zartaswa ta jiha da kuma Dattawan jam’iyyar PDP.